Fitaccen Jarumin finafinan Bollywood na kasar India Singh Rajput ya kashe kanshi ranar Lahadi da rana a gidanshi da ke Bandra a birnin Mumbai.
An sami gawarsa tana lilo a cikin gidansa da tsakiyar rana. Yanzu haka babu wani bayani dangane da dalili da ya sa dan shekara 34 Singh Rajput ya kashe kanshi.
Jarumin ya yi fice a wani shirin gidan Talabijin na Zee TV's 'Pavitra Rishta' a 2009 tauraruwarsa ta fara haskawa.
Haka zalika Jarumin ya dau hankalin masoyansa a fitaccen fim 'Kai Po Che!' na 2013, da kuma shirin finana finan soyayya kamar 'Shuddh Desi ' 2013, da kuma shirin finafinan fada kamar ' Byomkesh Bakshy!' na
2015..
Duniya za ta tuna shi da kyaun fuska da halittansa da ya sa dubban masoyansa ke begensa, a ciki da wajen kasar India.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari