Duba alamomi guda bakwai da za ka iya fara ji idan har ka kamu da ciyon zuciya

Ciwon zuciya ko bugun zuciya har yanzu shine na daya da yan Nijeriya suke fama dashi, inda hakan ya nuna cewar, a duk cikin mutane goma, uku na fama da ciwon.

Alamomin sun hada da, jin zafi a kirji da yawan yin zifa da jin kasala da wasu sauran alamau da za ku gansu a bayyana kamar yadda likitoci suka bayyana.

1. Kasala: Jin kasala tana daya daga cikin alamomin bugun zuciya musamman ga mata. Mutanen da zasu fara kamuwa da bugun zuciya zasu fara jin kasala kuma zasu ji sun kasa yin wani aiki. Aceawar kafar WebMD, hakan ya sanaya a lokacin bugun zuciya jinin dake zagayawa a zuciya yana raguwa da kuma sanya jin gajiya a damtse. Don ka kare lafiyar ka ya zama wajibi kaje kaga likita ba tare da bata wani lokacin ba don ya duba lafiyar ka.

2. Raguwa yin numfashi; Zaka dinga jin raguwar numfashin ka, alala misalai idan ka hau bene zaka dinga yin haki. In har kaji kana yin numfashi da kyar da jin gajiya bayan ka yi yar tafiya to wanana alamu ne na ka kamu da bugun zuciya. A cewar MayoClinic, zuciya tana taka rawa sosai wajen tura iska zuwa sassan jikin dan adam da kuma cirewa wasu sanadaran da jikin baya bukata.

3. Jin zafi mai radadi a zuciya: Idan kana jin zafi mai radadi a zuciya wanda kuma bai cika damun ka ba, ka tabbatar da ka tuntubi likitan ka domin wannaa alamu ne na bugun zuciya kumawannan alamar tana hana jinni yawo zuwa zuciya.

4. Gurbacewar ciki: Bugun zuciya wani lokacin yakan janyo lala cewar ciki kamar jin amai,inda hakan ya kan faru ne saboda wani irin abinci da kaci.

5. Fesowar kuraje a baya ko a damtsen hannu ko a cikin kirji: Jin zafi a wadanan wurare alamomi ne na an kamu da bugun zuciya kuma hakan yana janyo rashin fitar iska saboda jijiyon jinni sun rufe. Idan ka fara jin alamu ka tabbatar da kaje kaga likita.

6. Jin rashin sukuni a makogoro ko wuya ko a mukamuki: A nan zaka dinga jin rashin sukuni a makogwaraon ka ko a wuya ko kuma a mukamukin ka wanda kuma baka taba jin irin sa a baya ba, haka mutane m,asu fama da ciwon siga, sukan mayar da hankali a dukkan wani chanji da suka ji a jikin su.

7. Jin wani chanji gaba daya na ba dai dai ba a jiki: A ko da yaushe ka dinga sauraron wata murya da zaga dinga ji a cikin kanka, wananna ana yi maka gargadi ne. Wasu marasa lafiya su kan gayawa wasu likitocin su cewar basa ji sosai a saboda haka ya kamata ka tuntubi likita in ka fara jin hakan

al'ummata

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN