Dalilin da ya sa muka rasa kwanciyar hankali a rayuwa – Dakta Ahmad B.U.K

A wa’azin da gidan Rediyon DALA FM ke sa wa a kowacce safiya na Malamin Hadisi Dakta Ahmad Ibrahim B.U.K, a safiyar Larabar da ta gabata ya yi jan hankali ne bisa dalilin da ya hana mu samun kwanciyar hankali.

“Dalilin da ya sa muke shan wahala a rayuwa shine mun dauka kudi shine maganin kowacce matsala a rayuwa. Shi ya sa idan muka rasa su sai mu shiga matsala. Mun dauke su da matukar muhimmanci da idan muka ga mai kudi sai mu yi kamar mu bauta masa.

Abinda ba mu sani ba shine shi kudi ba shine maganin kowacce matsala ba, wani bangare ne na jin dadin rayuwa. Arziki ne kuma ba shi kadai ne arziki ba. Ba wai iyu ka ga Allah Ya hadawa mutum komai na rayuwa a duniya ba. Idan ya ba shi kudi kai ma akwai wani arziki da Allah Ya ba ka.

Shin Lafiya ba arziki ba ne? Ilimi ba arziki ba ne? Kyau ba arziki ba ne? Maikudi zai iya rasa lafiya kai Allah Ya ba ka. Maikudi zai iya samun ‘ya’ya su kangare masa Allah Ya Shirya maka naka. Duk abinda Allah Ya ba ka da za ka iya amfani da shi arziki ne. Sana’ar ka idan ka yarda da Allah ka yarda da ita sai Allah Ya daukaka ka a cikin ta.

Don haka ka nemi dukiyar Halak sai Allah Ya sa mata albarka fiye da dukiyar Haram. Ba yadda za a yi ka tara dukiyar Haram ka ce daidai take da dukiyar halak. Karamin ma’aikaci da ya ke cin halak sai ka ga ya yi hidimar gidansa hankali kwance, a aurar da wance a yi wancan. Idan yaro ba lafiya a jika wancan a ba shi ya warke. Idan ya sayo karamar atamfa ya Kawowa matarsa ta yi godiya ta sa albarka. Idan ta je shagon sayayya idonta kan kaya masu araha zai je a zo a sarrafa komai ya tafi daidai hankalinsu a kwance. Saboda Allah Ya sa albarka a dukiyar.

Amma wanda ya tara dukiyar Haram idan yaro ba lafiya sai an je private an je waje an kashe kudi. Idan ya zagaye garin nan ya sayo atamfar da ta fi kowacce sai shaidan ya kawar da idonta ta raina ta. Idan ma ta je gidan biki sai ta ga wacce ba ta kai tata ba amma ta ji ta fi tata. Idan ta je shagon sayayya idonta ba zai tsaya kan kananan abubuwa ba sai masu tsada. Haka zai yi ta kashe kudaden saboda Allah Ya cire musu albarka.

Sarki ne, Shugaban Kasa ne, Gwamna ne, ‘Yan Siyasa ne haka za su yi ta satar dukiyar Al’umma kuma Allah Ya hana su zaman lafiya a rayuwa. Sun saci kudaden kuma sun zagaye ko ina a duniya suna neman kwanciyar hankali amma sun rasa. Saboda Allah ba Ya barin zalinci. Ba su san ma yadda za su samu kwanciyar hankalin ba. Kuma kullum satar suke suna tara dukiyar.

Allah Ya ce abu Haramun ne kuma ka bi wannan hanya ka tara kudi ka ce daidai kake da wanda ya tara dukiyar Halak? Ba daidai suke ba.

Allah Ya Gafarta mana.. Ya sa mu dace

Daga Jaridar Alummata

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN