Jami'an yansanda sun ceto wani matashi daga tsunduma cikin Teku a 3MB da ke birnin Ikko watau Lagos.
Duk da yake yansandan sun hanashi yin tsalle ya tsunduma cikin Teku, matashin ya nuna bijirewav sai da kyar aka tafi da shi ofishin yansanda na Oworo inda yansanda suka tuntubi yanuwansa ta wayar salula.
Matashin ya yi ta furta kalamai masu nuna matsanancin damuwa da gajiya, tattare da bakin ciki kan rayuwa, lamari da ke manuniya cewa su ne dalilai da suka sa yake neman ya kashe kansa ta hanyar tsunduma cikin Teku.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari