Rundunar Soji ta kori Janar Hakeem Otiki saboda satar miliyoyin naira

An kori tsohon babban Kwamandan Rundunar Mayakar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto watau GOC, Manjo Janar Hakeem Otiki daga aiki.

Kotun wucin gadin da Hukumar Kula da Al'amuran sojoji ta kafa ne don yi masa shari'a kan sace wasu miliyoyin kudade mallakar rundunar ta yanke hukuncin.

Kotun karkashin jagorancin Laftanat Janar Lamidi Adeosun ta samu tsohon GOC din da laifi kan tuhuma biyar da ake masa.

An Otiki ne da satar Naira miliyan 100 da kuma Naira miliyan 160 mallakar rundunar sojojin Najeriya.

An kuma same shi da laifuka biyu na kin bin dokar rundunar soji karkashin sashi na 66 da Armed Forces Act (AFA).

Amma sai Hukumar Kula da Alamuran Sojojin ta amince sannan korar da aka masa za ta tabbata.

Rahotun Legit

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari