Duba abin da ke faruwa a Premier, La Liga da Serie A

A yayin da ake gab da dawowar wasa a gasannin Frimiya, La Liga da Serie A, kungiyoyi sun kara dukufa a kan kokarinsu na cimma mastaya da ‘yan wasan da suke shirin kawowa da za su cike musu guraban da suke fama da su.

Wasu kungiyoyin na shirin cinikin ‘yan wasa ne da za su rage musu yawan kashe kudade sakamakon tasirin cutar annobar coronavirus.

Ko a ina aka kwana a wannan makon?

—Manchester City na bukatar Chilwell

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta shirya tsaf domin shiga zawarcin dan wasan baya na Leicester City, Ben Chilwell zuwa lokacin da za a bude kakar sayen ‘yan wasa.

Dan wasan baya na kungiyar Leicester City, Ben Chilwell.
Dan wasan baya na kungiyar Leicester City, Ben Chilwell.

Jaridar Telegraph ta rawaito cewa kungiyar Chelsea ta dade tana bibiyar mai tsaron bayan dan shekara 23 amma City din na sa ran za ta iya dauko dan wasan.

Kocin City, Pep Guardiola ya fi mayar da hankali kan sanya Benjamin Mendy a bangaren baya ta hagu inda suke sauyawa da Oleksandr Zinchenko duk da cewa zai iya mayar da Zinchenko zuwa tsakiyar fili.

Euro miliyan 85 da kungiyar Leicester ta sanya wa dan wasan ka iya kawo tsaiko a kokarin da kungiyoyin ke yi na neman kawo shi ganin matsin tattalin arzikin da suka shiga.

—Neymar na son komawa Barca

Dan wasan gaba na Kungiyar Paris Saint Germain dan asalin kasar Brazil, Neymar De Silva ya bayyana wa takwarorinsa na kungiyar cewa yana son komawa Barcelona da ke Spaniya da taka leda.

Neymar wanda ya baro kungiyar a cikini da yafi kowanne tsada a duniya ya dade yana jan hankali a kafafen yada labarai inda Barca din ke sake zawarcinsa.

Dan wansan gaban Paris Saint-Germain Brazilian Neymar De Silva. Hoto: Getty Images.

Dan wasan mai shekara 28 ya nuna nadamarsa a fili na barin Barcelona tun watanni biyar bayan ya koma Faransa da taka leda a kan kudi Euro miliyan 222.

A baya-bayan nan jaridar Mundo Deportive to rawaito cewa kungiyar PSG ta gabatar wa Neymar din bukatar tsawaita kwantiraginsa zuwa shekarar 2022 lokacin da kwantiraginsa na yanzu zai kare.

Bayan kin amincewa da bukatar, Neymar ya kara fitowa fili ya bayyana rashin gamsuwar da zama a kungiyar.

Ya fada wa abokan wasansa na PSG cewa “Ina son komawa Barca, Eh kuma Eh”.

—Madrid na zawarcin Martinez

Dan wasan gaba na kungiyar Inter Milan, Lautaro Martinez.
Dan wasan gaba na kungiyar Inter Milan, Lautaro Martinez.

Gaza cimma matsaya tsakanin Lautaro Martinez da kungiyar Barcelona ta sanya kungiyoyin Manchester United da Real Madrid baje komarsu saboda shiga zawarcin dan wasan Inter Milan din.

 

Rahotanni daban-daban sun bayyana cimma wasu matakai cikin kokarin da dauko shi da Barcelona take yi.

Amma a baya-bayan nan Barcelona ta fara jan kafa saboda ganin ba za ta iya biyan faranshin Euro miliyan 99 da kungiyar ta kasar Italiya ta sanya wa dan wasan ba.

Jaridar Marca da ke Spaniya ta kuma rawaito cewa tattaunawa ta tsaya cik tsakanin bangarorin biyu.

Hakan ya sa kungiyoyin Real Madrid da Manchester United suka daura damarar shiga jerin wadanda suke zawarcin dan wasan idan har Barcelona ta gaza dauko shi.

—Tana kasa tana dabo a lamarin Pjanic

Dan wasan tsakiya na kungiyar Juventus, Miralem Pjanic
Dan wasan tsakiya na kungiyar Juventus, Miralem Pjanic

Dan wasan tsakiya na kungiyar Juventus ya ki amincewa da tayin da kungiyoyin Chelsea da Paris Saint Germain suka yi masa saboda sauya sheka inda ya jaddada bukatarsa ta komawa kungiyar Barcelona.

Jaridar Marca ta rawaito cewa dan wasan ya cigaba da kin amincewa da dukkanin bukatun da ake mika masa a makonnin da suka gabata saboda bukatarsa ta komawa Spaniya.

Kwantiragin dan wasan mai shekara 30 tare da Juventus zai kare ne a ranar 30 ga watan Yuni a kan kudi Euro miliyan 50.

Rahotun jaridar Aminiya
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN