Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tsarin karba - karba ne kadai zai nuna makomar yiwuwar takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
An fara maganganu a kasa a kan cewa Atiku zai fito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023. Adamu Atiku-Abubakar, ‘dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce mahaifinsa zai sake fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Jaridar Punch ta ce Alhaji Adamu Atiku-Abubakar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a jihar Adamawa. A makon da ya gabata ne Adamu Atiku-Abubakar ya shafe shekaru guda a ofis a matsayin kwamsishinan ayyuka a karkashin gwamnatin PDP ta Ahmadu Finitiri.
Da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a shekara guda, Adamu Atiku-Abubakar, ya yi magana game da siyasar Najeriya da kuma zaben 2023. Ya ce: “Ni a karon kai na, ban ga wani laifin mahaifina ya fito takarar kujerar shugaban kasa ba. A 2023, mahaifina (Atiku Abubakar) zai yi harin kujera mai darajar farko a kasar nan.”
Da ya ke bada dalilansa, sai ya ce: “Saboda (Atiku) ya kasance kwararren ‘dan siyasa, mai dabara, uban gida, wanda ya kuma lakanci harkar siyasa na kusan shekaru 40.” Atiku ya yi takarar neman kujerar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2019, amma sai ya sha kasa a hannun shugaba Muhammadu Buhari, dan takarar jam'iyyar APC.
Da ya ke magana yayin wani taro da manema labarai a Abuja, sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce; "PDP ba ta yanke wata shawara ba a kan tsarin karba - karba. Iya abinda zan iya fada kenan a halin yanzu."
Rahotun Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari