Yan sandan jihar Niger sun damke wani dan bindiga mai suna Ibrahim Muhammed.
Kakakin hukumar yansandan jihar Niger Wasiu Abiodun, ya ce yayin binciken ababen hawa na tsaya mu duba da yansanda suka yi a hanyar Minna zuwa Sarkin Pawa, yansanda sun tsayar da wani babur dauke da fasinja.
Bayan sun bincike kayan da aka dauko sai suka sami bindiga kiyar AK47 a wajen Muhammed wanda aka fi sani da suna Shagari Mayigyawa dan karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna. Ganin haka sai mai babur ya gudu ya shige gandun daji.
Kakakin yansandan ya kara da cewa Muhammed na cikin yan bindiga da ke addabar bayin Allah a garin Sarkin Pawa da Shiroro.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari