Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya canja me kula da tsaronshi inda ya
baiwa mataimakin kwamishinan ‘yansandan, Aliyu Abubakar Musa, mukamin.
Me baiwa shugaban kasar shawara ta musamman, Garba Shehu ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Yace shugaban yayi nadinne bayan canjawa tsohon babban metsaron nashi, Abdulkarim Dauda wajan aiki.
Hakan
na zuwa sati 2 kenan bayan dambarwar data faru tsakanin hadimin
shugaban kasa,Sabi’u Yusuf, wanda aka sani da Tunde Buhari da uwargidan
shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari