• Labaran yau


  Iran ta bayar da warantin kama shugaban Amurka Donald Trump sakamakon kashe janar Soleimani

  Gwamnatin kasar Iran ranar Litinin, ta bayar da Warantin kama tare da tsare shugaban Amurka Donald Trump da kuma fiye da mutum 30 sakamakon kashe Janar na kasarta Qasem Soleimani.

  Aljazeera ta labarta cewa mai shigar da kara na Gwamnatin Iran Ali Alqasimehr, ya ce hakan ya biyo bayan rawar da Trump tare da fiye da mutum 30 suka taka ne wajen hari da ya kashe Janar Soleimani ranar 3 ga watan Janairu. Sakamakon haka ya ce Trump zai fuskanci tuhumar kisan kai da ta'addanci.

  Amurka ta kashe Janar Soleimani a wajen birnin Baghdaza a wani harin soji da ta kai masa, lamari da ya haifar da zanga zanga a sassan Duniya.

  Saakamakon haka, zaratan sojin juyi juya hali na kasar Iran suka sha alwashin kai hari a maradun Amurka da Isra'la a yankin gabas ta tsakiya.

  Iran ta ce za ta bukaci taimakon yansandan kasa da kasa watau INTERPOL domin aiwatar da umarnin kama Trump. Haka zalika ta ce za ta ci gaba da bibiyan ganin ta kama tare da hukunta Trump ko bayan mulkinsa.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Iran ta bayar da warantin kama shugaban Amurka Donald Trump sakamakon kashe janar Soleimani Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama