Yadda Kasar China ke takurawa Musulman Uighur cin Alade da yin tsarin Iyali

Wasu sabbin Rahotanni sun bayyana cewa kasar China na takurawa musulman Uighur dake yakin Xinjiang yin tsarin haihuwa ba tare da son ransu ba.

Wani rahoto dag Daily Mail ya ruwaito wata mata, Zumret Dawud inda ta bayyana damuwa da cewa taje gurin Likita ya dubata, bayan an dubata kawai sai taji ashe ya daure mata mahaifane bata iya sake haihuwa.

Tace ta ji bacin rai sosai dan ta so ta sake samun da Namiji. Amma gashi yanzu ba dama.Rahoton ya kuma cewa ana tursasawa musulman Uighur cin Naman Alade a bikin Dragon Festival da ake duk shekara wanda bikine na masu bautar gumaka da shima ake tursasawa musulman halarta.

Rahoton da kungiyar kabilar Uighur dake kasar Jamus suka fitar yace a baya kasar China ta wa musulman kabilar kisan kare dangi.A cewar sanarwar duk wanda yaki yadda da sharuddan cin Naman Alade ana kaishi sansanin horo.

Hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN