Bayan kwanaki ana zanga-zanga sakamakon kashe-kashen mutane a jihar Katsina, Sifeto Janar na hukumar yan sanda, IG Mohammed Adamu, ya dira jihar tare da manyan jami'an gwamnatin Buhari.
Daga cikin wadanda ke cikin tawagar sune Dirakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi; mai bada shawara kan lamuran tsaro, Babagana Monguno; shugaban hukumar leken asirin kasa NIA, da sauran manyan jami'an yan sanda.
Daga dirarsu babban tashar jiragen sama, Umaru Musa Yar'adua, IGP na manyan jami'an sun garzaya gidan gwamnatin jihar domin ganawa da gwamnan Aminu Bello Masari.
Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai ya bayyana cewa manyan jami'an tsaron sun je Katsina ne domin shira rundunar hadin kai tsakanin Soji da yan sanda kan yadda za'a kawar da yan ta'adda a Katsina, Kaduna, Neja, Zamfara da Sokoto.
Rahotun Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari