Ba mu janye dokar kulle kwata-kwata ba – Inji Gwamnatin Kano


Gwamnatin jihar Kano ta musanta cewa ta janye dokar kulle kwata-kwata a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba shi ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da Aminiya a ranar Talata ta wayar salula.

Ya ce tun bayan sanarwar Gwamnatin Tarayya na sassauta dokar kullen da ta kakaba a jihar ranar Litinin, bisa ga dukkan alamu an sami rashin fahimta a tsakanin al’ummar jihar.A daren jiya ne dai gwamnatin jihar ta fitar da matsayinta ta bakin mai taimaka wa gwamna Ganduje a bangaren yada labarai, Salihu Tanko Yakasai inda ta ce za a bude dukkan kasuwannin jihar kuma harkokin kasuwanci za su ci gaba kamar yadda aka saba a da.

To sai dai sanarwar ta ce za a bude kasuwannin ne kawai a ranakun Laraba, Juma’a da kuma Lahadi, ba kamar yadda mutane suke tsammani ba.

Garba ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar damka ragamar yaki da cutar coronavirus ne a hannun jihohi ba wai janye dokar dungurungum ta yi ba.

Ya ce, “Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gwamnatin Kano ta amince mutane su ci gaba da harkokinsu a ranakun Laraba, Juma’a da kuma Lahadi kamar yadda aka saba.

“Za a ci gaba da amfani da wadannan ranakun har zuwa lokacin da za a sami ci gaba a yakin da muke yi da wannan annobar, amma dai kawo zuwa yanzu ba mu kai ga janye dokar gaba daya ba.

“Kasuwanni, wuraren ibada da na kasuwanci za su kasance a bude a wadannan ranakun.

“Muna sane da halin kuncin da wannan yanayin ya jefa jama’a ciki, amma muna so su fahimci cewa ba mai dawwama ba ne.

“Da zarar an samu ci gaba za mu janye gaba daya,” inji shi.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa zuwa yammacin ranar Talata gwamnatin za ta tattauna da kungiyoyin ‘yan kasuwa da shugabannin addini a jihar domin tsara yadda za a aiwatar da matakan kariya da zarar an bude wuraren ranar Laraba.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da kiyaye matakan kariya kamar amfani da takunkumin rufe fuska, wanke hannuwa a kai a kai da kuma ba da tazara a kasuwannin da sauran wuraren taruwar jama’a.

Binciken Aminiya ta gudanar ya gano cewa akasarin mutane sun fahimci wannan sanarwa a matsayin mai harshen damo, la’akari da wadda Gwamnatin Tarayya ta fitar tun farko kan dage dokar.

Hakan ya sa wasu suka yi tunanin cewa za su iya ci gaba da zirga-zirga a ragowar ranakun tun da dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire dokar, alabashshi sa fita kasuwannin a ranakun da aka sanar.

Aminiya ta lura cewa jami’an tsaro sun kasance a dukkan manya da kananan titunan birnin kuma sun kara kaimi wajen tabbatar da mutane sun ci gaba da bin dokar kullen tare da zama a gida in banda masu ayyuka na musamman.

Ya zuwa yanzu dai jihar Kano ita ce jiha ta biyu mafi yawan wadanda annobar coronavirus ta fi yi wa illa bayan Legas.

Rahotanni sun ce ya zuwa daren ranar Litinin, mutane 958 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, 240 kuma sun warke kuma an sallame su yayin da 45 kuma suka riga mu gidan gaskiya kamar yadda alkaluman ma’aikatan lafiya ta jihar suka tabbatar.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN