Type Here to Get Search Results !

Main event

Yadda uba ya yi wa diyarsa Jaririya yar wata bakwai fyade

Jami’an ‘yan sandan jihar Benuwai sun kama wani mutumi mai matsakaicin shekaru wanda ake zargin ya yi lalata da ‘yar cikinsa wanda ba ta wuce watanni bakwai da haihuwa ba.

Kwamishinan ‘yan sanda na Benuwai watau Mukaddas Garba ne ya shaidawa ‘yan jarida haka a garin Makurdi a lokacin da ya gabatar da wadanda ake zargi da laifin a gaban Duniya.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta fitar da rahoto cewa Mukaddas Garba ya gabatar da wannan mutumi da wasu mutum 104 a gaban ‘yan jarida a jiya Laraba, 3 ga watan Mayu, 2020.

Laifuffukan da ake zargin wadannan mutane fiye da 100 da su sun hada da garkuwa da mutane, fyade, fashi da makami, damfara, zamba cikin aminci, har ma da masu saba dokar kulle.

Mai girma kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa ya shirya yaki da tsagera, kuma zai yi bakiri kokarin na ganin ya batar da duk wasu miyagun mutane da ake adabbar jihar.

Mukaddas Garba ya ce ana zargin mutane 45 da aka kama da laifin shiga kungiyoyin asiri, 38 kuma za su amsa laifin fashi da makamai, sai wani guda da ake zargi da laifin damfara.

Har ila yau akwai mutane 4 da ake zargi da laifin garkuwa da mutane da su ka shiga hannun dakarun ‘yan sandan. Sannan Jami’an sun yi nasarar karbe makamai 15 da harsashai 20.

Daga cikin mutanen da aka kama ne aka samu wani mutumi mai suna Simon Emeka da ke aiki a sabuwar kasuwa wanda ake tuhumarsa da laifin kwanciya da ‘yarsa mai wata bakwai.

Da ya ke magana da ‘yan jarida, Simon Emeka, ya ce babu shakka malaman asibiti sun tabbatar da cewa an yi wa jaririyar ta sa fyade, amma ya ce babu hannunsa a wannan danyen aiki.

CP Garba ya ce ana cigaba da binciken Simon Emeka bayan ya shigo hannun hukuma a ranar 2 ga watan Yuni, 2020. A halin yanzu fyade ya zama ruwan dare a jihohi da-dama a Najeriya.

Rahotun Legit

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies