Rundunar yansandan jihar Akwa Ibom ta kori wani dansanda mai suna Mfon Esio daga aikin dansanda bayan ta sameshi da kasancewa dan kungiyar asiri.
An kori dansandan ne bayan bincike ya tabbatar cewa dansandan yana cikin yan kungiyar asiri na Junior Vikings Confroternity, wanda suka gudanar da aikin tsafinsu ranar 20 ga watan Mayu 2020.
Asiri ya tonu ne bayan an sace wani matashi mai suna Ubong John
William, kuma aka tilasta shi shiga kungiyar ta hanyar tilasta shi yin rantsuwar shiga kungiyar ta asiri.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari