Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Toungo da ke jihar ta Adamawa.
Karamar hukumar Toungo tana kudancin jihar Adamawa, kuma ta yi iyaka da kasar Cameroun.
Rahotanni sun nu8na cewa masu garkuwa da mutane suna tsakar raba kudin fansa na kusan naira miliyan ashirin N20m da suka karba daga wani attajiri, sai tsawa ta fada masu suka mutu nan take a wani daji.
Kakakin rundunar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce lamarin ya faru ne a yankin kasar Cameroun da ke iyaka da karamar hukumar Tougo a jihar Adamawa da ke Najeriya.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI