Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan
Yan Sanda Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar cafke wadanda ake zargi da yi
wa kananan Yara fyade da kuma luwadi har su sama da arba’in daga watan
Aprilu zuwa watan Yuni na wannan shekarar da muke ciki.
Kwamishinan ‘yan
sanda, Sanusi Buba, wanda ya samu wakilcin Kakakin rundunar ‘yan sanda
SP Gambo Isa, a lokacin da yake baje kolin masu laifin a helkwatar
rundunar da ke Katsina.Wadanda aka kamo masu aikata wannan muzgunawa
kananan Yara maza da mata, an kamo su daga kananan hukumomi talatin da
hudu na jihar Katsina.
Kuma akwai masu mabanbanta shekaru ne. Akwai masu
shekaru sittin da biyar har zuwa ashirin. Akwai wanda ya yiwa kanwarsa
fyade wanda suke uba daya. Akwai kuma wadanda suke da wani rukuni, wanda
kowa sai ya yi lalata da wadanda suka samu.
Akwai wani Mai waka yabo,
da ake zargi da dauko wani yaro daga garin su Abukur, ya kawo shi cikin
garin Katsina, yana lalata da shi ta Dubuta. Akwai dan shekara ashirin
da ya yiwa yar shekara biyar fyade.
Duk a cikin su akwai dan shekara
sittin da biyar da ya lalata kananan yara guda ukku. Mafi yawancinsu sun
amsa laifukkan su.Kwamishinan ya ce da zaran an kammala bincike za a
maka su gaban kuliya manta sabo, wasu kuma tuni an fara gurfanar da su
gaban kotu. Kuma ya yi kira ga iyaye su dunga kula da suwa yayansu ke
mu’amala ta yau da kullum.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari