Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe kofin Premier League a daren
yau bayan Chelsea tawa Manchester City 2-1 a wasan da suka buga a daren
yau.Christian Pulisic ne ya fara ciwa Chelsea kwallo inda Kevin De
Bruyne ya farketa.
Willian ya ciwa Chelsea kwallon daga kai sai gola
bayan da Fernandinho ya taba kwallo da hannu wadda tasa aka bashi jan
kati.Shekaru 30 kenan Rabon Liverpool da Kofin wanda a wannan shekarar
ta lashe bayan ta yi nasara a wasanni 28 cikin 30 data buga.
Har yanzu
akwai sauran wasanni 7 da zata buga wanda hakan yasa ta kafa tarihin da
babu kungiyar data taba kafashi, a baya dai Manchester United da City
sun lashe kofin Premier League da sauran wasanni 5 da za’a buga.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari