Yansanda jihar Kano sun damke wani mutum mai shekara 32 mai suna Mohammed Alfa a garin Kwanar Dangora bisa zargin aikata fyade.
Ana zargin Alfa da aikatawa mata 40 fyade ciki har da tsohowa mai shekar 80 a Duniya.
Kakakin yansandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da labarin, ya kara da cewa ana yawan samun karuwar aikata fyade a garin Dangora, lamari da ya saka jama'a cikin fargaba, kafin dubun Mohammed Alfa ta cika.
Wata mata ce ta kama shi a cikin dakin yaranta, amma sai ya gudu, kuma jama'a suka bi shi suka kamashi ranar Talata 9 ga watan Yuni.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari