Ababe 12 da ya kamata miji ya kula kafin ya auri mace domin kaucewa bakin ciki a zaman aure

Akwai ababe da dama da ya kamata na miji ya kula da su idan zai auri Mace, ko da budurwa ce ko Bazawara.Wadannan ababe sune halaye da suka bayyana ga Mace yayin hulda na yau da kullum.

Ba babban bakin ciki ga rayuwar Namiji kamar yin kuskuren auren Mace da bata da tarbiyya, biyayya ko ragowa ga Miji a zamantakewar aure.

Ga wasu ababe da ya kamata ka kula da su kafin ka auri Mace.

1. Idan kana magana da budurwa ko Mace, kuma tana yawan kallonka kai tsaye a cikin adanunka, sai ka yi taka tsantsan domin za ta yi maka fiye da haka idan ka aureta.

2. Budurwa ko macen da bata iya hada ido da kai idan kuna zance, tana jin kunyan hada ido da kai ita ce mace da ya kamata ka ba muhimmanci.

3. Ka sake tunani a kan duk Budurwa ko Macen da take daga muryarta fiye da naka idan kuna zance, ko idan kana magana sai ta jefa magana ta haka sai ta hana ka ci gaba da naka zance sai dai nata. Wannan ya kamata ka kula zata baka wahala idan ta zo gidanka.

4. Burdurwa ko Mace da ke gaya maka cewa " Karya kake yi" idan kuna zance, zata yi maka dozin na kalaman rashin ragowa idan ka aure ta.

5.  Budurwa ko mace da bata cewa " Yi hakuri" idan har ka nuna cewa ta yi maka laifi, sai ka kula domin idan ka aureta ba mamaki hatta tuwo sai ka je ka dauko wa kanka balle ruwan wanke hannu.

6. Budurwa ko Mace da bata yafewa idan ka yi mata laifi, ko wani ya yi mata laifi sai ta rama kafin hankali ya kwanta, Malam ka yi nisa da kawo irin wannan mata a gidanka dasunan aure. Domin zo mu zauna zo mu saba inji Bahaushe. Idan babu yafiya kuwa, zama zai yi wuya ya daure.

7. Idan Budurwa ko mace na yawan dora maka lalurar anko, sayen ababe masu tsada ko wani abin da ba wajibi ba, lallai alamu ne na cewa ba mamaki idan ta zo gidanka za ta nemi samun fiye da haka, sai ka shirya.

8. Ka nisanci macen da take yawan korafi a kan abokanka, yanuwanka, ko danginka. Zai yi wuya ka rayu hankali kwance ba tare da zumunci da su ba.

9. Ka rabu da Budurwa ko Mace da ke yawan yi maka tsaki idan kuna zance, domin wannan alaman rashin tarbiyya ne daga iyayenta, ko ta koyi wani hali da baya da kyau daga kawaye. Idan ka aureta, za ta yi maka fye da haka a gidanka.

10. Kada ka yi wa Budurwa ko mace alkawarain cewa ba za ka kara wani aure ba idan ka aureta. Mata da yawa na amfani da wannan dalili kafin a yi aure, idan miji ya saba kuma ya zama dalilin tayar mashi da hankali a gidansa bisa cewa ya saba alkawarin cewa ba zai yi mata kishiya ba.

11. Ka kula idan Budurwa na fita daga gidansu babu sa ido ko kulawa daga iyayenta, babu shakka idan ka aureta ba za ta yarda ta zauna a gida kawai ba. Zancen zuwa biki, wajen kawaye da makwabta shi ne zai kawo maku damuwa.

12. Ka kula Budurwa ko Mace da ita ce ke sonka ba wai kai ne ke sonta ba, idan da hali, Malam ka koma kanta kai tsaye, domin za ka fi samun biyayyar aure da kwanciyuar hankali bisa wacce kai ne ke wahalan sonta.

Isyaku Garba Zuru

Alhamis 11, Yuni, 2020.
  
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN