Rahotun JaridarAminiya
Wata babbar kotu da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara ta
yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi mai suna Kamal
Yusuf bayan samun shi da laifin kashe mahaifiyarsa da kuma kannensa mata
guda biyu.
Gwamnatin jihar Zamfara ce dai ta gurfanar da matashin a gaban kotun
jihar tare da wasu mutum biyu da suka hada da: Armaya’u Shehu da kuma
Caleb Humphrey akan aikata laifuffuka guda uku.
To sai dai daya daga cikin wadanda ake tuhuma din mai suna Caleb Humphrey ya mutu yayin da ake sauraren shari’ar.
Laifukan
dai sun hada da: hada baki domin aikata laifin fashi da makami da kuma
aikata kisan kai wanda kuma hukuncinsa kisa ne matukar an samu wanda ake
zargi ko tuhuma da aikata hakan.
Da take yanke hukuncin, babbar jojin jihar ta Zamfara mai shari’a
Kulu Aliyu ta samu Kamal Yusuf da aikata laifukan ta kuma yanke mashi
hukuncin kisa ta hanyar rataya, a yayin da kuma ta wanke Armayau Shehu
daga dukkan zargi ta kuma sallame shi.
Idan
dai za a iya tunawa a shekarar dubu 2013 aka kama Kamal Yusuf da
abokansa su biyu bisa zargin kisan mahaifiyarsa Hajiya Hafsatu da kuma
kannensa mata guda biyu wato Maryam da Amina.
Kamal ya yi fushi da mahaifiyar tashi bayan da taki yarda ta bashi
dukiyar da kannensa suka gada daga mahaifinsu, wanda ta aura bayan
rabuwarta da mahaifin Kamal.
Kamal ya gayyato abokansa suka kuma kashe mahaifiyar tashi da kannensa, suka jefa gawarwakinsu a cikin babban Dam na Gusau.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari