Kurtun dansanda ya harbe matarsa ya kuma harbe kanshi da bindiga, karanta dalili

Wani jami'in dansandan kasar Kenya mai suna Michael Siwalo da lambar aiki 116272 ya kashe kanshi da bindigarsa ta aikin dansanda bayan ya harbe matarsa ranar Juma'a.

Kurtun dansanda daga garin Buuri ta kudu da ke gundumar Meru, ya harbe matarsa mai suna Silvia Ramat Letei a ciki da bindigarsa na aikin dansanda da misalin karfe 6:15 na yamma, kafin ya juya bindigar ya harbe kanshi.

Lamarin ya faru ne sakamakon wata hatsaniya na cikin gida da aka samu tsakanin kurtun dansandan da kuma matarsa a gidansu da ke shiyar Panama a Timau da ke gundumar Meru.

Rahotun yansanda ya ce Letei tana cikin mawuyacin yanayi kuma an kwantar da ita a Asibitin Nanyuki.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN