• Labaran yau


  Dokar taron ibada: Kotu ta ci tarar limaman Juma’a biyu a Bauchi, duba yawan kudin

  Rahotun Jaridar Aminiya

  Wata kotun tafi-da-gidanka a Bauchi ta yanke wa wasu limamai biyu hukuncin biyan tara ta N20,000 ko wanne, bayan ta same su da laifin jagorantar sallar Juma’a a masallatai daban-daban.

  An gurfanar da limaman, Malam Musa Hassan da Malam Dahiru Alhaji, a gaban kotun ne ana tuhumar su da yin karan tsaye ga dokar gwamnatin jihar ta hana taruwa a wuraren ibada.

  Duk su biyun dai a kauyen Dunkui Ambi na karamar hukumar Misau suke.

  Kotun, a karkashin jagorancin Alkalin Majitare Muktar Abubakar, ta ce ba za ta yi wa duk wanda aka samu yana saba wa dokar jihar ta hana wasu harkoki da sauki ba.

  Alkali Abubakar ya yi kira ga al’ummar jihar su yi biyayya ga umarnin hukumomi.

  A yanzu haka dai gwamnatin jihar ta Bauchi ta haramta tarukan jama’a, ciki har da taruka a wuraren ibada, a yunkurin hana kwayar cutar coronavirus yaduwa.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dokar taron ibada: Kotu ta ci tarar limaman Juma’a biyu a Bauchi, duba yawan kudin Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama