• Labaran yau


  Yanzu yanzu: Dakarun sojin Bataliya ta 29 na gwabza fada da yan boko haram a Mainok

  Dakarun sojin Najeriya da ke Mainok a karamar hukumar Kago na jihar Borno na gwabza fada ta hanyar musanyar wuta yanzu haka da yan kungiyar boko haram.

  Mazauna yankin sun ce yan boko haram sun isa kauyen da misalin karfe 7 na yamma suka dinga harbin mai uwa da wabi kuma suka doshi sansanin sojin inda soji suka fuskance su da martanin gaske.

  Rahotanni sun ce sojin Bataliya ta 29 ne ke gwabzawa yanzu haka da yan boko haram a Mainok yayin da kauyawan yankin suka nemi mafaka.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yanzu yanzu: Dakarun sojin Bataliya ta 29 na gwabza fada da yan boko haram a Mainok Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama