• Labaran yau


  Tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10

  Rahotun Legit Hausa

  Wata kotun tarayya da ke zamanta a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta ci tarar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) miliyan goma a kan tsare wani matashi, Anthony Okolie, na tsawon sati goma ba bisa ka'ida ba.

  A shekarar 2019 ne hukumar DSS ta kama matashin Okolie bayan ya cigaba da amfani da wani layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi.

  Duk da matashin ya gabatar da shaidar sayen layin bisa ka'ida, hukumar DSS ta tsare shi bisa zargin yana amfani da layin wajen mu'amala da mutane da sunan Hanan. Zargin da Okolie ya musanta

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama