Yan Jarida 55 sun mutu a kasashe 23 sakamakon cutar coronavirus tun 1 ga watan Maris

Kungiyar gangamin yancin yan Jarida  The Press Emblem Campaign (PEC) ta ce, yan Jarida 55 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar coronavirus a fadin Duniya a watanni biyu da suka gabata.

Kungiyar ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta fitar gabanin ranar yancin walwalan yan Jarida na Duniya World Press Freedom Day wanda za a yi ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce mafi yawan yan Jaridar na aiki cikin yanayi mai hadari musamman wajen fuskantar matsalar cutar coronavirus, duk da yake  cewa mafi yawansu basu da cikakken kariya da kayan aiki don fuskantar yanayin.

Sanarwar ta kara da cewa tun ranar 1 ga wata Maris, PEC ta hada adadin yan Jarida 55 da masu aikin samar da labarai a kasashe 23 da suka rasa ransu, sakamakon kamuwa da cutar coronavirus yayin da suke gudanar da aikinsu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN