Yadda Ministoci biyu suka kamu da Korona

Mutum 5,000 sun kamu da cutar korona a kasar Chile kamar yadda mahukunta a kasar suka sanar a ranar Litinin 25 ga watan Mayun shekarar 2020.

Cikin sabbin mutum 5,000 din da suka kamu da cutar har da ministocin gwamnatin Shugaban kasa Sebastian Pinera. Hukumomin lafiya sun sanar da sabbin wadanda suka kamu da cutar 4,895 a kasar da ke nahiyar Amruka ta Kudu inda suka ce cutar ta kashe mutum 43.

Ministan Ayyuka, Alfredo Moreno da Ministan Makamashi Juan Carlos Jobet sun ce suna cikin wadanda suka kamu da cutar.

 "An sanar da ni cewa na kamu da kwayar cutar COVID-19 kwanaki kadan da suka gabata amma dai ba ni da alamomin cutar kawo yanzu," a cewar Moreno a shafinsa na Twitter.

Ministan mai shekaru 63 a duniya ya ce ya killace kansa bayan daya daga cikin maaikatansa ya kamu da cutar. Jobet shima ya kamu da cutar bayan ya fara killace kansa a ranar Asabar,

"A lokacin da ya fara jin alamomin da ke da alaka da cutar," a cewar sanarwar da maaikatan makamashin ta fitar. Sanarwar ba ta fayyace yadda ministan mai shekara 44 ya kamu da kwayar cutar ba amma ta ce, "bai yi cudanya da shugaban kasa Sebastian Pinera ba ko wani jamian gwamnatin a baya bayan nan.

" Wasu ministocin uku da suka killace kansu saboda sunyi cudanya da wadanda ke da cutar sun koma aiki bayan sakamakon gwajin ya nuna ba su kamu ba.

An makon da ta gabata ne aka samu mutane masu yawa da suka kamu da cutar a kasar wadda hakan ya saka gwamnatin kasar ta saka dokar kulle a Santiago. Babban birnin jihar ce inda annobar ta fi yaduwa inda kashi 90 cikin 100 na mutum 74,000 da suka kamu suka fito.

A makon da ta gabata, majalisar kasar ta tafi hutun dole bayan sanatoci uku sun kamu da coronavirus. Yanzu an cigaba da zaman majalisar ta hanyar amfani da intanet

Rahotun Legit

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN