Matan Ogoni sun gudanar da zanga zanga rabi tsirara a jihar Rivers

A ranar yau matan Ogoni a jihar Rivers, sun gudanar da zanga zangar lumana bisa abin da suka kira ci gaba da tsare Manajan Otal na Prudent da Gwamnatin jihar Rivers ta rushe karkashin jagorancin Gwamna Nyesome Wike ranar 10 ga watan Mayu take yi.

Ranar Litinin ne Gwamnatin jihar Rivers ta sanar cewa Manajan Otel na Prudent da aka rushe watau Bariledum Azoroh yana cikin wadanda suka kamu da cutar Korona a jihar, sakamakon haka aka killace shi tare da wadanda suka kamu da cutar.

Sai dai wani na hannun daman mai Otal da aka rushe mai suna Promise Gogorobari, ya musanta cewa Bariledum Azoroh ya kamu da cutar Korona, yace yana nan lafiya kalau, kuma Gwamnati ta tsare shi ne ba bisa ka'ida ba.

Sakamakon abin da ya faru ya sa matan suka tube rabin jikinsu suka rike kwalaye da ke dauke da rubiuce rubucen neman Gwamnati ta saki Bariledum Azoroh.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari