Ta hanyar waka na sami duk abin da nake so, inji Maryam Fantimoti

Maryam Fantimoti mawakiya ce da ta shafe tsawon lokaci tana sana’ar.

Hakan ne ya sa ake yi mata lakabi da Maman Mawaka a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.

A wata hira da ta yi da Aminiya kwanan baya, ta bayyana yadda ta fara harkar waka da yanayin rikon amana a tsakanin masu wannan sana’a.

Wace ce Maryam?

Sunana Maryam Saleh Muhammad, wadda aka fi sani da Fantimotin Waka; a Kano aka haife ni.

A nan na yi aure na haifi ‘ya’ya uku. Wakar da nake yi ma a Kano na faro ta, yau ga shi na zo Legas, kuma na je garuruwa da dama na yi waka.

Yaya aka yi kika samu kanki a sana’ar waka?

Kusan zan iya cewa a cikin sana’ar waka na tashi, domin na fara wake tun ina ‘yar shekara takwas a makarantar Islamiyyarmu da ke unguwar Gyadi-gyadi a Kano.

A wancan lokaci da wakokin begen Annabi Muhammadu (SAW) na faro kuma har gobe a kan wannan turba na dasa harsashin wakena, wato wakokin addinin Musulunci.

Na shiga yin wakokin nishadi ne saboda sha’awa, na kuma nuna bajinta a wannan fanni.

Wannan ne dalilin da ya sa na shiga Kannywood a tsakanin 1999 zuwa 2000 domin ni lokacin da na shigo masana’antar akwai masu ba da raino.

Ka ga ni Ali Nuhu ne ya karbe ni, kuma ya gwada ni sai ya kai ni wajen Yakubu Muhammad lokacin shi ne Sarkin Mawaka, sai ya ba ni wakar nan da na ci sunanta kuma har zuwa yau nake amsa sunanta wato ‘Fantimoti’.

Kuma har ila yau ana yin wannan waka, ita tasa na yi suna, kuma shi kansa Ali Nuhu da ya ga haka bai sanya wakar a fim ba sai ya ce bari ya ajiye ta a matsayin tarihi tun da sunanta ya bi ni.

A wancan lokaci akwai yarda da amana, ba kamar yanzu ba.

A lokacin da na yi waccan wakar Ali Nuhu ya kai wa marigayi Tijjani Ibrahim sai ya ce, “Wannan muryar babu irinta, don haka an samu canjin Zuwaira Isma’il”.

Saboda ni muryar Zuwaira na ji na shigo waka lokacin da suka yi wakar ‘Dawayya’ ita da Misbahu M. Ahmad, to ita ta jawo ni, don na ga ni ma fa mawakiya ce a Islamiyya, don haka ni ma zan iya.
Amma kuma sai na zo da salo na tatsuniya; da na rubuta na kawo wa Ali Nuhu sai ya ce ai ni murya ta ita ce makamina.

Saboda haka tun daga nan ban kara waiwayar biro ko takarda da zimmar rubuta waka ba, sai dai duk inda na samu sarari kawai rerata zan yi.

Kuma da yake akwai kula ta magabata sai na ci gaba da samun nasara, don ka ga bayan Yakubu ya raine ni sai Mudassiru ya dora.

Allah Ya saka musu da alheri; ba zan iya mantawa da su ba a rayuwata.


Kuma da yake akwai kula ta magabata sai na ci gaba da samun nasara, don ka ga bayan Yakubu ya raine ni sai Mudassiru ya dora.

Allah Ya saka musu da alheri; ba zan iya mantawa da su ba a rayuwata.

Ko kin fuskanci kalubale lokacin da kika shiga sana’ar waka gadan-gadan?

Ka san ita rayuwa gaba dayanta cike take da kalubale, ballantana a sana’a wadda Allah Ya ba ka nasibi a cikinta.

Akwai kalubale da dama, amma da arzikin Allah da addu’a sai ka ga duk ya wuce.

Yau sama da shekara 21 kina waka, ko akwai bambanci tsakanin wancan lokaci da yanzu?

Ai abin sai dai a ce ma sha Allah, la haula wa la kuwwata illa billah, saboda ka ga yanzu ci gaba ya zo.
Lokacin da muke yi a baya babu kwamfuta, babu faifan sidi sai tape recorder, amma yanzu alhamdulillahi al’amura sun zo da sauki.

Yanzu lokaci ne na baje kolin wakoki a intanet, ko ke ma kin shiga wannan mataki?

A gaskiya zuwa yanzu ban shiga matakin baje kolin wakokina a kafafen sadarwar zamani ba.
Ba na sanya wakokina a YouTube ko Instagram ko Facebook ko makamantan haka.

Domin yanzu amana ta yi karanci duk wanda ka ja a jiki domin ya zo ku yi wani abu tare sai ka ga yana kokarin ya ci amana ko ya dakushe ka.

Amma har gobe ina ci gaba da gudanar da al’amurana kamar yadda nake yi a baya, domin idan ka yarda da Allah ka yi ikhlasi duk inda kake ko a rami ne arzikinka zai zo ya riske ka.

Ko wane alfanu kika samu a shekarun da kika yi kina waka?

Na samu amfani da yawa wadanda lokaci ba zai ba ni damar fada ba — duk wani alfanu da ake samu a waka ni ma na samu.

Kuma babban abin da nake alfahari da shi shi ne yadda wakar ke sada ni da masoyina fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

Baya ga haka na yi tafiye-tafiye da dama a dalilin waka yanzu ma ita ce ta kawo ni Legas zuwa bikin cikar Sarkin Fulanin Legas Alhaji Muhammadu Bambado shekara 25 bisa karagar mulki.

Na zo na yi masa waka kuma Allah Ya hada ni da kai wakilin Aminiya a Legas, ka ga wannan ma alfanu ne da kullum nake samu saboda waka.

Rahotun Aminiya
 
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN