Al'umma Musulmi a koina cikin fadin jihar Kebbi sun gudanar da ibadar watan Ramadana domin neman yardar Allah kamar kowane Musulmi a Duniya. Haka zalika masu hannu da shuni ko masu rike da manyan mukamai a Gwamnatance a jihar sun bayar da taimako ga bayin Allah mabukata. Amma fa da yawa daga cikin irin wadannan taimako sun hadu da cikas kafin su kai hannun talakawa.
Wani lamari mai ban haushi daga daya daga cikin irin wadannan misalai shine yadda wani bawan Allah, babban dan siyasa mai mukami. ya bayar da kyautar Naira dubu dari biyu N200,000 domin a kai ma wani Limami a matsayin Sadaka. Amma sai mai kai sako ya wawure Naira dubu dari da ashirin N120.000 ya kai wa Limami N80,000.
Bayan Liman ya sami sakon, sai ya daga wayar salula ya shaida wa dan siyasa cewa "Ranka ya dade na ga sakon N80,000 Allah ya kara arziki, na gode, Allah ya saka da alkhairi"
Amma sai dan siyasa ya ce " Nawa aka kawo maka? sai Liman ya ce N80.000" Daga bisani dan siyasa ya aje wayar salularsa. Saidai bayani da muka samu ya nuna cewa dan siyasa bai yi komai ba domin ganin an mayar wa Liman N180,000 da mai kai sako ya zalunce shi.
Haka zalika, akwai bauyanin yadda aka ba wani mutum kayakin Azumi domin taimaka wa bayin Allah, amma sai wanda kayakin suka biyo ta hannunsa ya yi ta aikata abin son ra'ayinsa komabayan abin da uban gidansa ya bukata ayi da kayakin
SHARHI
Mujallar ISYAKU.COM na kira ga duk dan siyasa, mai hali ko hannu da shuni, manyan jami'an Gwamnatin jihar Kebbi wadanda suka taimaka wa bayin Allah cikin watan Ramadana, su gudanar da bincike yadda aka raba kayaki da suka bayar domin neman yardar Allah a watan na Ramadan.
Mujallar ISYAKU.COM ta bankado gagarumin rashin imani da wasu maketatan bayin Allah da ba su ne suka bayar da kayakin ba, kuma ba daga aljihunsu aka samar da dukiya da aka cire aka sayi abin da aka bukaci talaka ya amfana da shi ba, amma sun zama shamakin ga aikin alkhairi daga mutanen alkahairi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari