Harin bam ya kashe mutum shida a Somaliya
Mutum shida sun mutu, da dama kuma suka samu raunuka yayin da wani bam ya tashi a gefen hanya a Somaliya.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar zuwa birnin Mogadishu babban birnin ƙasar daga garin Afgoye.
Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa bam din ya tashi ne yayin da wata ƙaramar mota ƙirar bas ke tafiya kan hanyar.
Duk da babu kungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai ƙungiyar Al Shabab ta kai hari ga motoci a yankin a kwanakin baya.
An kashe mutum 20 a wata kasuwar shanu
WaÉ—anda suka shaida lamarin sun bayyana cewa Æ´an bindigar sun zo ne da tsakar rana inda suka buÉ—e wuta ga jama'ar kasuwar da ke a lardin Kompienga.
Sai dai har yanzu babu tabbaci kan kungiyar da ta kai harin. A 'yan kwanakin nan, ana samun yawaitar hare-hare musamman na masu iƙirarin jihadi da kuma rikicin ƙabilanci a ƙasar.
A farkon shekarar nan, yawan waɗanda 'yan bindiga suka raba da muhallansu a ƙasar ya ƙaru daga dubu 90 zuwa sama da dubu 800.
Tun a 2017, rikici a ƙasar ya tilasta wa makarantu su rufe a arewacin ƙasar.
Za a buÉ—e wasu makarantu a Ingila gobe Litinin
Wasu daga cikin yara dalibai za su koma makaranta gobe Litinin a Ingila, sai dai babbar tambayar da jama'a ke yi a ƙasar ita ce ko akwai wani haɗari tattare da wannan matakin?
Bincike ya nuna cewa a fadin Birtaniya, kashi 0.01 cikin 100 na waɗanda suka mutu a ƙasar yara ne ƴan kasa da shekara 15.
Kashi 1 cikin 100 kuma matasa ne ’yan shekara 15-44, sai kuma kashi 75 cikin 100 na waÉ—anda cutar ta kashe sun wuce shekaru 75.
Sai dai duk da waɗannan alƙaluman, wasu makarantun ba su goyon bayan buƙatar gwamnatin ƙasar na makarantu su koma aiki.
Zanga-zanga: An saka dokar hana fita a sama da birane 12 na Amurka
Birane fiye da goma sha biyu ne aka ƙaƙaba wa dokar hana fita a Amurka yayin da zanga-zangar tarzoma ta ci gaba a dare na biyar, kan kisan da 'yan sanda suka yi wa Ba'amurke ɗan asalin Afirka, da ba ya dauke da makami, George Floyd.
Birane a ƙalla talatin ne zanga-zangar ta fantsama cikinsu a faɗin ƙasar. Masu zanga-zanga sun kara da ƴan sanda a wurare da dama ciki har New York da Miami da Philadelphia da kuma Los Angeles.
An cinna wuta kan motocin ƴan sanda tare da yin amfani da duwatsu don jifan jami'an tsaron da ke harba hayaƙi mai sa hawaye da gurnetin hargitsa lissafi da harsasan roba. Kuma a rana ta biyu, masu zanga-zanga sun taru a fadar White House da ke birnin Washington.
An gudanar da Sallar Asuba a Masallacin Madina ranar Lahadi
Mutum 553 suka kamu da korona ranar Asabar a Najeriya
A wani abu da ba a taɓa gani ba tun bayan ɓullar annobar korona a Najeriya, hukumomin ƙasar ranar Asabar sun ba da rahoton gano mutum 553 da cutar ta sake harba.
Da wannan tashin zabi na alƙaluman masu cutar, ƙiris ya rage yawan masu korona ya cilla zuwa 10,000.
Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka ta Najeriya ta fitar a daren Asabar sun nuna cewa adadin masu korona yanzu 9,855 a ƙasar.
Alƙaluman sun kuma nuna cewa mutum 12 cutar ta yi sanadin mutuwarsu a ranar.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari