Yadda aka kashe wani dansanda wajen aiwatar da dokar hana zirga zirga

Wasu bata gari a jihar Edo sun kashe wani dansanda mai suna Felix Egbon bayan sun harbe shi da bindiga ranar Juma'a 8 ga watan Mayu da dare, lokacin da yake gudanar da aikin tabbatar da dokar hana zirga zirga na Gwamnatin tarayya.

Kakakin rundunar yansandan jihar Edo Chidi Nwobuzor ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar 9 ga watan Mayu. Ya ce dansandan da aka kashe yana aiki ne a ofishin yansanda na Auchi kafin a kashe shi, bayan an kai masu farmaki tare da sauran yansanda da suke aiki.

Ya kara da cewa an garzaya da Felix zuwaa Asibitin Central Hospital da ke garin Auchi, amma aka tabbatar da mutuwarsa.

Yanzu haka yansandan jihar Edo sun dukufa wajen farautar wadanda suka yi wannan aika aika da niyyar kamo su domin fuskantar hukunci.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN