Kamar yadda muka saba daga lokaci zuwa lokaci mukan zakulo
maku yanyoyin da zaku kara samun lafiyar jikunnan ku musamman ma ta hanyar
anfani da abubuwan dake zagaye da mu.
Yau ma kuma gamu dauke da alfanun 'ya'yan iccen nan bakake
na dinya da kan nuna musamman ma a irin wannan lokacin na tsakiyar damina
Dinya dai da ake kira da Black plump juice a turance icce ne
da kan fito a gonakin mutane kuma tana yin girma sosai sannan kuma tana fitar
da bakaken 'ya'ya a tare da ita dake kama da na kanya.
1. Tana taimakawa wajen gyaran ciki da muka maganin
matsalolin da ke tattare da hakan kamar gudawa.
2. Tana maganin cuwalwatan da suka shafin hakora da ma baki
gaba daya.
3. Tana maganin dankanoma da basir mai tsiro.
4. Tana maganin tari da kuma cutar Asuma.
5. Tana maganin mura da kuma karin karfin garkuwar jiki.
DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari