• Labaran yau


  Mutum 1 ya kamu da Korona Gwamnatin jihar Katsina ta sa dokar hana zirga zirga a Ingawa

  Gwamnatin jihar Katsina ta sa dokar hana zirga zirga a karamar hukumar Ingawa bayan sakamakon gwajin DCDC ya nuna cewa mutum daya ya kamu ta cutar Korona a kamaramar hukumaar.

  Sakataren Gwamnatin Katsina Mustapha Inuwa ya ce dokar za ta fara aiki ne daga karfe 7 na safe ranar Asabar 10 ga watan Mayu.

  Tun farko dai jihar Katsina ta rufe iyakarta da jihohin Kano, Kaduna, da kuma Jamhuriyar Nijar. Daga cikin kananan hukumomi 34, kawo yanzu kananan hukumomi 12 suna karkashin dokar hana zirga zirga.

  Kananan hukumomin su ne Daura, Dutsinma, Katsina, Mani, Safana, Kankia, Matazu, Musawa, Jibia, Batagarawa, Malumfashi da Ingawa.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 1 ya kamu da Korona Gwamnatin jihar Katsina ta sa dokar hana zirga zirga a Ingawa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama