Wata mata mai juna biyu ta mutu sakamakon cutar coronavirus a jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wata mata mai dauke da juna biyu sakamakon cutar coronavirus, wanda ya kawo yawan adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar a fadin jihar zuwa mutum biyu.

Kwamishinan Lafiya na jihar Jigawa Abba Zakari ne ya sanar da haka. Ya ce " Jihar jigawa ta sami mutuwar mutum na biyu sakamakon cutar coronavirus, mace mai juna biyu daga karamar hukumar Miga, wacce ta mutu sakamakon zuban jini bayan ta yi bari yayin da take cibiyar killacewa da ke Dutse".

Ya kara da cewa tun farko an kwantar da matar a Asibitoci biyu, kafin a same ta da cutar coronavirus. Tuni aka binne matar bisa tsarin dokokin addinin Musulunci.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN