An kama matar da ke jinyar cutar coronavirus da ta tsere daga wajen killacewa a Taraba

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin jihar Taraba ta ce ta damke wata majinyaciya da ta tsere daga cibiyar killacewa ta jihar bayan an tabbatar tana dauke da cutar coronavirus. Wacce aka damke din mai suna Talatu Idris an kama ta ne tare da mayar da ita cibiyar killacewa.

Kwamishinan lafiya na jihar kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar, Dr Innocent Vakkai ya bayyana hakan a Jalingo, babban birnin jihar a ranar Litinin. Ya bayyana cewa an fara zakulo wadanda suka yi ma'amala da masu cutar a jihar don hana yaduwarta.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, kwamishinan yace za a kara yi wa majinyatan cutar na jihar wani gwajin don sanin halin da suke ciki. Ya kara da musanta rade-radin cewa an bude makarantu da wuraren bauta na jihar. Kamar yadda yace, "Makarantun mu da wuraren bauta za su ci gaba da zama a rufe.

Ana shawartar jama'a da su ci gaba da kiyaye dokokin hana yaduwar cutar a kwanaki biyun da ake barin zirga-zirga a jihar." Ya kara da cewa jihar ba za ta ba almajiran da aka kawo daga wata jihar masauki ba har sai an tabbatar da cewa basu dauke da muguwar cutar.

A halin yanzu, jihar Taraba na da mutum 8 da ke dauke da cutar coronavirus kuma ta wajabta saka takunkumin fuska na kwanaki biyun da take barin walwalar jama'a a jihar. A gefe guda, gwamnatin Katsina ta bayar da umarnin sake rufe wasu manyan kasuwannin uku da ke ci sati - sati a jihar. Sakataren gwamnatin jihar Katsina,

 Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu. Kasuwanni da wannan umarni ya shafa sune; Garkin Daura, Dusti, da Kayawa. An rufe kasuwannin ne bayan gwamnati da ma su ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu a kan hauhawar mutanen da ke kamuwa da cutar covid-19 a jihar Katsina.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post