COVID-19: An kama mutum 155 da suka saba dokar kulle a Sokoto

Rahotun Legit Hausa

Rundunar Yan sanda ta jihar Sokoto ta kama mutum 155 daga karfe 8 na daren ranar Laraba zuwa karfe 6 na ranar Alhamis da suka saba dokar kulle da aka saka a jihar don dakile yaduwa annobar COVID-19.

Wannan na cikin wata sanarwa ce ta mai magana da yawun rundunar, Muhammad Sadiq, mai mukamin mataimakin superintendent na yan sanda ya fitar a ranar Alhamis a Sokoto kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

 Mr Sadiq ya ce twagar hadin gwiwa ta jamian tsaro karkashin jagorancin kwamishinan Yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Mayu ta kama motoci da babura a kalla 63

Ya ce, "An gudanar da ingattacen binciken a kan kamen da aka yi kamar yadda kwamishinan yan sanda ya bayar da umurni kafin a kai su kotu." Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kama duk wani mutum ko kungiya ta aka samu da saba dokar ta hana fita.

"Ina kira ga alummar Sokoto su rika biyaya ga doka tare da bin shawarwarin da hukumomi suka bayar su rika zama a gidajen su da dadare domin an saka dokar ne saboda dakile yaduwar kwayar cutar a jihar."

A wani rahoton, kun ji cewa Wakana Enan Ngari, Kansilar da ake nema ruwa a jallo a kan zargin satar shanu da wasu laifufuka a jihar Adamawa ya mika kansa hannun Yan sanda a karamar hukumar Numan na jihar. DSP Suleiman Nguroje,

Mai magana da yawun rundunar yan sanda na Adamawa ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis a Yola kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Nguroje ya ce an tafi da kansilar da ake zargi zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar (CID) domin cigaba da bincike. Nguroje ya ce,

 "Rundunar yan sandan jihar Adamawa tana son sanar da alumma cewa Kansila mai wakiltan mazabar Vulpi a karamar hukumar Numan ya mika kansa ga yan sanda."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN