• Labaran yau


  Trump: Zamu jaye tallafin Amurka kuma mu fice daga WHO domin kai dan amshin China ne

  Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar jaye tallafin kudi da Amurka ke ba Hukumar kula da lafiya ta Duniya ta Majalisar dinkin Duniya (WHO) domin yaki da cutar Korona.

  A wata takarda da Trump ya aika wa shugaban Hukumar Lafiya ta MDD,  Tedros Ghebreyesus ranar Litinin 18 ga watan Mayu, Trump ya yi zargin cewa WHO tana jan kafa wajen tafiyar da aikin dakile cutar  tun watan Disamba.

  Ya kuma yi zargin cewa WHO na da alhakin yawancin wadanda suka mutu sakamakon cutar Korona tun lokacin da ta bulla. Sakamakon haka ya ce tilas a yi habbaka ko Amurka ta jaye tallafi da take bayarwa kan matsalar cutar har abada, kuma Amurka za ta duba yiwuwar ficewa gaba daya daga kungiyar.

  Trump ya yi zargin cewa shugaban WHO Tedros Ghebreyesus, dan amshin shatan kasaar China ne.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Trump: Zamu jaye tallafin Amurka kuma mu fice daga WHO domin kai dan amshin China ne Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama