Mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu Riek Machar tare da matarsa Angelina Teny, wacce ita ce Ministan tsaro, sun kamu da cutar Korona .
Wannan sanarwar ta fito ne daga ofishinsa ranar Litinin 18 ga watan Mayu, sanarwar ta kara da cewa wasu daga cikin masu tsaron lafiyarsa sun kamu da cutar tare da wasu ma'aikatan ofishinsa.
Hakazalika Machar ya tabbatar da wannan zance a wani hira da ya yi a gidan Talabijin , ya kara da cewa zai killace kansa a gidansa har tsawo kwana 14 tare da masu yi masa hidima da suka kamu da cutar.
Sudan ta kudu tana da mutum 347 da suka kamu da cutar Korona, yayin da mutum shida suka mutu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari