Har da dan Nijar cikin Almajiran da Kano ta mayar jihar Kebbi

Wani yaro dan asalin Jamhuriyar Nijar na cikin almajirai da gwamnatin Jihar Kano ta tusa keyansu zuwa jihar Kebbi.

Yaron mai shekara bakwai da haihuwa na cikin almajirai 83 da ke rukuni na biyu da gwamnatin Kano ta mayar da su Kebbi a matsayin jiharsa ta asali.

Kwamishinan lafiya jihar kebbi, Mohammed Jafar yayin karbar korarrarun almajiran a garin Birnin Kebbi, ya ce jiharsa ci gaba da rike almajirin har sai an damka shi ga iyayensa a kasarsu.

Ko da yake bai fadi dalilin sanya yaron mai shekara bakwa dan kasar Nijar a cikin almajiran jihar kebbin ba.

Tuni dai gwamnatin jahar ta Kebbi ta damka korarrun almajiran ga shugabbanin kananan hukumominsu na asali domin damka su ga iyayensu.

Almajiran da jihar Kano ta dawo da su sun fito ne daga kananan hukumomin, Birnin-kebbi, Kalgo, Dandi, Argungu, Maiyama, Jega da kuma Yauri.

Jafar, wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar, ya kara da cewa kafin gwamnatin Kano ta dawo da yaran, sai da aka yi musu gwaji aka kuma tabbatar ba su dauke da wata cuta.

“Dukkan almajiran nan da aka dawo da su daga jihar Kano, an yi musu gwajin Covid-19 kafin maido su jihar kebbi. Sakamakon gwajin nasu ya kuma nuna cewa babu mai dauke da cutar.

“Akwai kuma yaro almajiri dan shekara bakwai wanda kuma dan Jamhuriyar Nijar ne a cikin wanda gwamnatin jihar Kano ta dawo da shi jihar Kebbi.

“Gwamnatin Kebbi za ta ci gaba da kula da shi har sai ta samu cikaken bayanai na yadda za a gano iyayensa a can kasarsu.”

Wanna dai shi ne karo na biyu da jihar Kebbi ke karbar ayarin korarrun almajiranta daga jihar kano.
Rahotun Aminiya

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN