• Labaran yau


  Sojin Britaniya 3 sun shiga uku bayan sun tube zindir suka dau hotuna akan jirgin sama

  Wasu sojin Britaniya guda uku sun shiga uku bayan sun tube zindir suka dauki hoto a kan wani jirgi da aka yi wa suna Red Arrow domin tunawa da wasu sojin sama guda biyu da suka mutu. Sojin suna aikin tafiyar da kariya ne wajen gwajin Korona a unguwar Lincolnshire.

  Daya daga cikin sojin mai suna Colour Sergeant 'Tats Taylor ne ya saka hotunan a shafinsa na Facebook wanda hakan ya ja Allah wadai daga jama'a.

  Sauran sojin da ke cikin hotuna sun hada da Corporal Shane Woods da Private Anthony Panton

  Kakakin sojin Britaniya ya ce za a dau matakin horo a kan wadannan soji, saboda sun saba dokar tarbiyyan sojin Britaniya.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sojin Britaniya 3 sun shiga uku bayan sun tube zindir suka dau hotuna akan jirgin sama Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama