Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani Janar na soji bayan ya karya dokar hana zirga zirga ko sa takunkumin fuska sakamakon cutar Korona.
Kwamishinan shrai'a na jihar Kaduna Aisha Dikko ce ta sanar da haka a Kaduna ranar Litinin 18 ga watan Mayu.
Ta ce " Hafsan sojin ya fito ne daga Abuja sanye da Khakinsa, tare da wasu mutum uku wadanda basu sanye da takunkumin fuska. An tuhume shi kuma aka same shi tare da sauran mutanen da laifin karya dokar hana zirga zirga da rashin sa takunkumi.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani Limami Mai suna Yusuf Rigachukun tare da danshi sakamakon karya dokar hana zirga zirga sakamakon cutar Korona.
An kama Malamin ne a Shataletalen Jami'ar jihar Kaduna (KASU) domin bai sa takunkumin fuska ba tare da danshi. Ya bayar da uzurin cewa kafar sadarwar Kaduna State edia Corporations ce ta gayyace shi domin ya gabatar da wani shirin Rediyo.
Aisha Dikko ta ce " An tuhumi Rigacukun tare da danshi da laifin rashin sa takunkumi kuma aka ci su tarar N5000 kowanensu".
Ta kara da cewa Kotun tafi da gidanka ta kuma umarci Malamain ya gabatar da wani shiri da zai fadakar da jama'a hanyoyi da jama'a za su bi domin su kare yaduwar cutar Korona"
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari