• Labaran yau


  Soji da dansanda sun harbi juna da bindiga bisa tunanin yan ta'adda ne

  Sojin kasar Kenya guda biyu tare da wani jami'in dansandan kasar, sun yi wa junansu mumunan raunuka bayan sun buda wa juna wuta da bindigogi bisa tunanin cewa yan ta'adda ne a Bura da ke yankin Garissa.

  Rahotanni sun ce Kurtun dansanda Emmanuel Ngao ya harbi jami'an soji guda biyu David Mbugua da Jeremy Malusi bayan an sami zafafan cacan baki lokacin da suke zagayawan sintiri, sai suma suka mayar da martani suka harbe shi.

  Shugaban yansandan Fafi George Singalao ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce an kai jami'an soji da na yansandan Asibitin Bura cikin mawuyacin yanayi sakamakon raunukan harbin bindiga.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Soji da dansanda sun harbi juna da bindiga bisa tunanin yan ta'adda ne Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama