A yayin da masana kimiya da mahukuntan lafiya a duniya ke ci gaba da rige-rigen samar da maganin cutar korona, mun ji cewa wata kungiyar masu bincike a kasar Indonesia ta cimma wani munzali na nasara.
A ranar Alhamis wata kungiyar kwararru masu bincike a kasar Indonesia, ta bayyana cewa ta gano sunadarai a cikin wasu kayan amfani na gona da ke da ikon yakar cutar korona.
Dr Ari Fahrial Syam, wani kwararren masanin cututtuka a Jami'ar Indonesia, ya ce sunadarin hesperidin, myricetin, luteolin da kuma casuarinin duk ana samun su a jikin 'ya'yan jar Gwaiba.
Dr Syam ya ce dukkanin wannan sunadarai su na taka rawar gani kuma sun wadatu da ikon magance cutar korona.
- Kamar yadda jaridar aa.com.tr ta wallafa, kwararren masanin kiwon lafiyar ya ce sakamakon bincikensu ya nuna cewa, wannan sunadarai da ake samu a jikin 'ya'yan Gwaiba su na iya hana kamuwa ko kuma rage tasirin cutar korona.
Da ya ke ganawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency, Dr Syam ya ce bishiyar Gwaiba ta na fitowa ko ina a kasar kuma ana iya cin 'ya'yanta kai tsaye ko kuma idan an sarrafa sun zama ruwan abun sha na 'ya'yan itatuwa.
A halin yanzu kungiyar kwararru wadda Dr Syam ya ke jagoranta da kuma Cibiyar Noma ta Bogor, su na neman hadin gwiwar kamfanonin harhada magunguna domin samar da maganin cutar korona daga jikin 'ya'yan Gwaiba.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Dr Syam ya ce kungiyarsu sai ta yi gwajin wannan magani a jikin dabbobi da mutane domin tabbatar da ingancin sa gabanin ya samu karbuwa a duniya.
Wata hazika a fannin kiwon lafiya daga Cibiyar Noma ta Bogor, Irmanida Batubara, ta ce ba bu shakka sunadarin hesperidin yana da ikon ba wa jiki kariya da riga-kafin kamuwa da kwayoyin cututtuka na microbes da viruses.
Baya ga Gwaiba, Batubara ta ce ana samun sunadarin hesperidin a bawon lemun zaki, na lemun tsami da na lemun taba da sauran dangin kayan lemu wanda a turance ake kira citrus.
Ta ce mutane za su iya hada ruwan 'ya'yan itatuwa na sha su na zaune a gidajensu sannan kuma su jefa bawon lemu da aka tabbatar da tsaftar, kuma su jefa a ciki.
Sai dai da ya ke 'Yan Hau
sa ne cewa, "Hanyar Lafiya a bi ta da shekara", Batubara ta ce sunadarin hesperidin ya na da dandano mai daci kadan.Rahotun Legit
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari