Rahotun BBC Hausa
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad
Sa'ad Abubakar na III ya ce sai ranar Lahadi za a yi Sallar Idi a
Najeriya sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal a kasar.
Saboda haka ranar Asabar za ta zama rana ta 30 ga watan Azumin Ramadan."
Hakan ne ya sa Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Majalisar Koli ta Addinin Musulunci suka yanke cewa ranar Lahadi 24 ga watan Mayu wadda ta yi daidai da 1 ga Shawwal 1441 ce ranar Idi a Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da kasar Saudiyya ta ce ba ta ga jaririn watan Shawwal ba a saboda haka za a yi Sallah ne ranar Lahadi.
Ita kuwa makwabciyar Najeriya, Jmahuriyar Nijar ta sanar da ganin watan na Shawwal inda za a yi Idi a ranar Asabar.
Ba wannan ne karon farko da ake samun babban ba tsakanin kasashen duniya dangane da ganin wata na fara Azumin Ramadan da kuma karkare shi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari