Kungiyar Ulamas ta ce Ganduje ya tafka ganganci sakin mutane da yayi su gwamatsu zuwa sallar idi

Rahotun Premiumtimes Hausa
Shugaban Kungiyar Ulamas na jihar Kano Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya yi gangancin janye dokar hana zuwa masallatai a jihar da kuma sassauta dokar domin a tafi masallacin idi.
Ibrahim Khalil ya ce gwamna ganduje bai shawarce su ba kafin ya janye dokar.
” Da gwamnati ta tuntube mu tabbas da mun gaya mata gaskiya cewa lokaci bai yi ba a bude masallatai da kuma sakin mutane su gwamatusu zuwa masallacin idi.
” Tabbas da mun gaya wa gwamna cewa lafiyar mutane na da muhimmanci sosai, kuma da ya duba abin da kyau kafin ya janye wannan doka. Mu dai ba a shawarce mu ba.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya janye dokar hana sallar juma’a sannan Kuma ya amince a yi sallar idin karamar Sallah idan an ga wata ranar Asabar ko Lahadi.
Kakakin gwamnatin jihar Kano, Salihu Tanko ya shaida cewa gwamna Ganduje ya gana da manyan malamai 30 a jihar na sama da awa biyu. A karshen ganawar gwamnatin jihar ta amince amince a janye dokar hana sallar juma’a a jihar sannan kuma idan Allah ya kai mu ranar Asabar ko Lahadi za a yi sallar idi.
” Gwamnati ta amince al’umma su halarci sallar Idi ranar sallah a duk fadin jihar. Sai dai ya ce a bi ka’idojin da gwamnati ta saka domin kiyaye kamuwa da cutar Korona.
” An umarci Malaman Masallatan Juma’a da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka takunkumin fuska ya kuma wanke hannaye da saka sanadarin tsaftace hannaye sannan a raba sahu kuma kuma a saka jami’an hizba su tabbata an bi wadannan dokoki.
Idan ba a manta shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar Zaman Gida Dole a jihar Kano da mako biyu. Wannan amincewa ta fito daga shugaban kwamitin Dakile yaduwar cutar Korona, Boss Mustapha ranar Litini.
Dama kuma gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar da mako daya.
A wannan taron manema labarai shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.
Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.
” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.
” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.
CORONAVIRUS: Ku saurari sabbin matakai daga Buhari ranar Litini – Boss Mustapha
Wannan Sanarwa ya shafi jihar Kano da a makonni biyu da suka gabata shugaba Buhari ya saka dokar ‘Zaman Gida Dole’ a dalilin barkewar annobar korona a jihar.
Wannan doka dai ya nuna cewa jihohi da dama ba za su samu damar zuwa sallar Idi ba idan allah ya kai mu an kammala azumin watan Ramadan.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN