• Labaran yau


  Samun masu covid-19: Gwamnatin Katsina ta sa dokar hana zirga zirga a Malumfashi

  Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya sa dokar hana fita a garin Malumfashi daga karfe 7 na safe ranar Alhamis 7 ga watan Mayu.

  Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa ne ya sanar da haka, ya ce Gwamnati za ta yi sassauci ga shagunan sayar da kayan abinci, magunguna da ayyukan jinkai.

  Wannan ya biyo bayan samun wasu mutane dauke da cutar koronavirus a wannan yankin.

  Dokar ta bukaci jama'a su yi biyayya ga dokoki domin kauce wa fushin jami'an tsaro ga duk wanda ya ki bin doka.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Samun masu covid-19: Gwamnatin Katsina ta sa dokar hana zirga zirga a Malumfashi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama