Covid-19: An kai Sarkin Daura asibitin Katsina da gaggawa an garkame Fadarsa

An garzaya asibiti da Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk kuma a ka kwantar da shi a sashen wadanda ake ba kulawa na musamman a asibitin FMC Katsina ranar Talata  biyar ga watan Mayu.

Daily Trust ta ruwaito cewa an dauki Sarkin ne da karfe 1 na dare kuma aka tafi da shi Katsina.

Wata majiya ta shaida wa Nigerian Tribune cewa jikin basaraken ya tsananta ne , sakamakon haka aka dauke shi cikin gaggawa aka tafi da shi Asibiti a Katsina.

Haka zalika bayanai sun ce an garkame Fadar basaraken a halin yanzu. Dr Mustapha Inuwa, Sakataren Gwamnatin Katsina ta tabbatar da garkame Fadar Sarkin Daura bayan an sami mai dauke da cutar Coronavirus..

Ana fargaban cewa kila Sarkin ya kamu da coronavirus domin Likitansa Marigayi Aminu Yakubu ya yi hulda da Sarkin tare da Matarsa Hajiya Binta Umar bayan ya dawo daga tafiya kuma ya mutu sakamakon cutar coronavirus.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari