• Labaran yau


  Rikakken dan boko haram ya yi saranda ya mika kansa ga sojin Najeriya

  Fitaccen dan kungiyar boko haram Yahaya Adamu wanda aka fi sani da suna Saad Karami ya mika kansa ga jami'an sojin Najeriya.

  Shelkwatan sojin Najeriya ta fitar da sanarwar haka ranar 29 ga watan Mayu.

  Haka zalika sanarwar ta ce Yahaya ya tuba ne kuma ya mika kansa ga jami'an sojin dakaru na Barikin 242 Munguno ranar 24 ga watan Mayu.

  Yahaya ya ce yana cikin wadanda suka jagoranci hari da aka kai wa jami'an soji a Baga, haka zalika yana cikin wadanda suka kai hari a Metele, Mairari, Bindiram, Kangarwa da Shetimari a cikin jamhuriyar Nijar.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rikakken dan boko haram ya yi saranda ya mika kansa ga sojin Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama