Wanda aka kama mai suna Sansari Ojha dan shekara 70 kuma Limamin addinin gargajiya na wajen bauta na Dei ya sare kan dattijo Saroj Kumar Pradhans da adda a cikin wajen bauta.
Ya gaya wa yansanda cewa ubangijin gargajiyarsa ne ya umarce shi a cikin mafarki cewa ya kashe dan adam kuma ta haka ne zai kawo karshen cutar Korona a kasar India.
Sai dai yansanda sun ce Ojha ya kashe Saroj ne da dare ranar Laraba a cikin wajen bauta bayan an sami zafafar cacan baki a tsakaninsu.
Dansanda mai bincike Ashish Kumar Sigh ya ce Ojha ya kai kansa ofishin yansanda a yanayi da ya nuna buguwa da barasa, kuma ya shaida masu abin da ya aikata.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari